Dalibai 624,000 sun amfana da tallafin NELFUND a jami’o’i 239

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Lamunin Ilimi ta Nijeriya (NELFUND) ta bayyana cewa ta raba naira biliyan 116 domin biyan kuɗin makaranta da kuma tallafin kula da ɗalibai a faɗin Nijeriya.

Manajan Darakta na NELFUND, Akintunde Sawyerr, ya bayyana haka a wata hira da ‘yan jarida a Abuja, inda ya jaddada ƙudurin gwamnatin tarayya na tabbatar da ilimi mai rahusa da shigar da kowa cikin tsarin ilimi a matakin jami’a da kwalejojin ilimi.

Sawyerr ya bayyana cewa daga cikin wannan adadi, biliyan N65 an biya kai tsaye zuwa ga jami’o’in gwamnati 239 a madadin ɗaliban da suka samu amincewa da lamuni.

Sauran N51 biliyan kuma an bai wa ɗaliban a matsayin kuɗin kula da su a kowane wata.

“Jimillar adadin lamuni da aka karca ya kai 1,067,000, daga cikin su 624,000 sun riga sun amfana da tsarin. Mun biya kuɗin makaranta da kulawa ga ɗalibai a jami’o’i da kwalejoji 239 na gwamnati. Jimillar biliyan N116 ne aka raba, kuma mutane da dama sun amfana da wannan tsarin,” inji Sawyerr.

Shugaban NELFUND ya ce tsarin lamunin ilimi na daga cikin manyan shirye-shiryen saka hannun jari na zamantakewa na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, domin kawar da matsalolin kuɗi ga ɗaliban makarantu, ta yadda babu ɗan Nijeriya da za a hana shiga tsarin ilimi saboda rashin kuɗi.

A kan dalilin da ya sa ba a biya kuɗin makarantar sabbin zalibai ba, Sawyerr ya ce haɗarin asarar kuɗi ne babba.

Ya bayyana cewa akwai yiwuwar ɗalibai waɗanda ba su yi rajista ko matriculate ba su iya canza ra’ayi, ko su canza makaranta, wanda zai sanya gwamnatin ta fuskanci asarar biliyoyi.

“Idan muka biya kuɗin makaranta ga waɗanda ba su shiga makaranta ba, me zai faru idan sun canja ra’ayi ko ba su je makarantar ba? Ba za mu iya kawai mu ce a biya da zarar an samu gurbin kararu ba, sai dai za mu biya kafin ranar rantsarwa ba,” inji Sawyerr.

By ukarofi