Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa Jam’iyyar APC ce ta bar shi ba shi ne ya barta ba.
El-Rufai a hira da ya yi da DW Hausa, ya zargi jam’iyya mai mulki ta APC da yi masa rufa-rufa da kuma baɗa masa hayaƙi bayan sun tura motar ta tashi.
Daga nan sai ya ƙara da cewa ”Ko ɗa ne kake da shi ya ki yi maka biyayyaka yi masa komai amma ya ƙi biye maka, za ka tsine masa ka bar shi da duniya, haka APC, na tsine mata na barta da duniya.
Game da ziyarar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a Kaduna, El-Rufai ya ce bayan sun tafi ne shi ma shugaban APC Abdullahi Ganduje ya kai wa tsohon shugaban ziyara.
”Ai ziyarar Ganduje ga Buhari neman suna ne kawai da iyayi, amma ba shine ya ke yi wa Buhari shaguɓen ‘Habu Na Habu ba’ ya riƙa yi masa ‘izgilanci’ amma yanzu wai ya ziyarce shi.
El-Rufai ya ƙara da cewa ya zaɓi jam’iyyar SDP ne saboda ta na da manufofi irin na taimakon al’umma da talakawa.
“Jam’iyyar SDP ta yi kama da irin jam’iyyar da za mu yi tafiya a ciki domin taimakon talakawa da mutanen mu na Arewa musamman da ƙasa baki ɗaya
El-Rufai tare da wasu gaggan ‘yan jam’iyyun adawa na shirin dagula wa jam’iyya mai mulki lissafi a wata sabuwar tafiya wanda suka kira sabuwar goguwar canji.
