
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamishinan ƴan sanda na tawagar jami’ai na musamman, CO Abayomi Shogunle ya bayyana dalilan da suka sa aka tsare ɗan jarida kuma mai fafutukar ƴancin al’umma, Omoyele Sowore da hukumarsu ta yi.
Kwamishinan ya ce, an kama Sowore da tsare shi ne bisa umarni kan zargin sa da ƙin bada bayani a lokacin da jami’an ƴan sanda suke bincike akan wasu al’amura da suka shafe shi.
Shogunle ya bayyana haka ne yayin wani jawabi ga masu zanga-zanga da ƴan jarida a Abuja, ranar Juma’a.
Da fari Sowore ya amsa gayyatar Sufeton ƴan sanda ɓangaren sanya ido a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Laraba, inda daga bisani aka tsare shi.
Akan haka ne magoya bayan Sowore suka tsunduma zanga-zanga a sassan jihohin Legas, Abuja, Osun, da Oyo inda suke kira da sako shi.
Hallau, a kwanan nan ne Sowore ya jagoranci zanga-zangar nuna buƙatar samar da walwala ga jami’an ƴan sandan da suka yi ritaya, ya kuma yi tsokaci masu nauyi akan shirin ƙarin matsayi a hukumar.
