Ƙungiyar ‘yan sanda na duniya wadda a ke kira da INTERPOL ta bayyana cewa sa’a ɗaya miliyoyin daloli a fitar wa daga Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika.
Ƙungiyar ta bayyana harkar halasta kuɗin haram ya ƙaru sosai a wannan shekarar musamman a ƙasashen mu na Afirka wanda dole sai hukumomin tsaro sun tashi tsaye sannan za su yi maganin wannan abun.
Garba Baba Umar wanda shine mataikin shugaban na Afirka shi ya bayyana hakan a yayi buɗen wani taron ƙarawa juna sani da aka shiryawa jami’an ‘yan sanda da ke Nijeriya.
Umar ya cigaba da cewa dole a tashi tsaye a yaƙi wannan lamarin saboda duk wani kuɗi da ya shigo ko ya fita zai zama barazana ga ƙasa ta fannoni daban-daban.
Cikin wanda suka halarci taron harda shugaban hukumar EFCC wanda ya ce a wannan lokaci dole hukumomin tsaro su haɗa kawunansu domin a magance matsalar.
Haka ma itama Hafsat Bakare wadda itace shugabar hukumar NFIU, ta yi kira da dole sai an tashi tsaye ta hanyar ƙarawa juna sani musamman tsakanin hukumomin da abin ya shafa domin ganin an magance matsalar.
