Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Lauyar ’yar ƙasar Maroko, Khadija Diab, ta ce matar ba ta tare da malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, kamar yadda mijinta ya yi zargi.
Lauyar, Bilkisu Abdulrasheed Chedi, ta ce Khadija ta koma Maroko tun watan Afrilun 2026, kuma tun daga wannan lokacin take zaune tare da iyalanta.
Chedi ta ce ƙungiyarta, Women Aware of Rights Initiative, ta taimaka wa Khadija wajen samun takardar tafiyar gaggawa bayan da mijinta, Nasiru Idris Musa, ya riƙe fasfo ɗinta.
Lauyar ta bayyana hakan ne a wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook na Sheikh Gumi, yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan inda matar take.
Ta ce Khadija ta tuntuɓi ƙungiyar a watan Oktoban 2025, inda ta zargi mijinta da cin zarafinta a gida, rashin isasshen abinci da kuma wasu nau’o’in musgunawa.
Chedi ta ce daga baya an kai Khadija asibiti domin yi mata gwaje-gwaje, inda sakamakon ya nuna cewa ta kamu da wasu cututtukan da ke da alaƙa da jima’i.
A cewarta, Khadija daga bisani ta bayyana cewa ba ta son ci gaba da zaman auren.
An shigar da ƙara a madadinta a Kotun Shari’a da ke Kaduna a watan Oktoban 2025.
Sai dai shari’ar ta samu tsaiko sakamakon buƙatar yin sulhu, sauya lauyoyi da kuma ƙalubalantar ikon kotun na sauraron shari’ar.
Chedi ta ce daga baya Khadija ta shiga damuwa, sannan ta nemi komawa gida Maroko.
Saboda haka, ƙungiyar ta taimaka mata wajen samun takardar tafiya, bayan zargin mijinta da riƙe mata fasfo.
Ta ce hukumomi da Ofishin Jakadancin Maroko da ke Nijeriya sun tabbatar da cewa Khadija ta isa ƙasar lafiya kuma tana tare da iyalanta.
Lauyar ta ƙara da cewa Khadija ta ba ta izinin ci gaba da jagorantar shari’ar a madadinta.
An dakatar da shari’ar farko a watan Yunin 2026, yayin da aka sake shigar da wata ƙara a watan Yuli domin neman raba auren bisa doka.
Chedi ta buƙaci jama’a su yi watsi da zargin cewa Sheikh Gumi ya tsare Khadija, inda ta jaddada cewa matar ta koma Maroko tun watan Afrilun 2026 kuma tana zaune tare da iyalanta.
