Dan ƙunar baƙin wake ya ya kashe sojoji biyar a Borno

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tarwatsa bom, inda ya halaka sojoji biyar a garin Pulka da ke ƙaramar Hukumar Gwoza a jihar Borno.

Mazauna yankin da kuma majiyoyin tsaro sun ce lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi a wani shingen binciken sojoji.

Wata majiya ta ce ana zargin maharin ɗan ƙungiyar ISWAP ne, wanda ya daɗe yana ɓuya a tsaunukan Mandara.

Majiyar ta ce, “Wasu sun bayyana cewa ya kwana kusa da shingen sojojin yana shirin aikata wannan mummunan aiki.

“Da safe, lokacin da aka buɗe hanya ga masu wucewa, sai ya yi kamar ɗaya daga cikinsu, ya tayar da bam a cikinsu. Sojoji biyar suka rasa rayukansu nan take.”

Wani mazaunin yankin ya ce, “Tun fiye da shekara guda kenan, wannan shi ne kawai harin ƙunar baƙin wake da aka samu a nan. Wannan na nuni da bukatar sabuwar dabarar jami’an tsaro don kauce wa maimaituwar hakan.”

Wannan sabon hari ya tunatar da munanan tarihin hare-haren ƙunar baƙin wake da aka taɓa kai wa a Gwoza da sauran sassan jihar ta Borno.

Ko a ranar 30 ga watan Yunin 2024, wasu mata biyu ’yan ƙunar baƙin wake sun tayar da bama-bamai a wajen bikin aure a garin Gwoza, inda suka kashe mutane 18 ciki har da yara da wata mace mai juna biyu.

Haka kuma, a ranar 21 ga watan Yuni, 2025, akalla fararen hula 11 suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata, lokacin da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a wajen kallon wasan kwaikwayo a ƙaramar Hukumar Konduga.

By ukarofi