Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bankin Shigo da Kayayyaki na Afirka (Afreximbank) ya sanar da rattaɓa hannu kan wata yarjejeniyar bayar da tallafin Dala biliyan 1.35, domin tallafa wa kamfanonin Dangote.
Yarjejeniyar wata ɓangare ce ta kusan Dala biliyan huɗu da aka haɗa ta hada-hadar kuɗaɗe na Dangote, babbar cibiyar masana’antu ta Afirka. Afreɗimbank ya yi aiki a matsayin mai tsarawa ne.
A cewar wata sanarwa da Blueprint Manhaja ta gani, “Wannan tallafin – ɗaya daga cikin manyan lamuni na hada-hadar kuɗi a kasuwannin hada-hadar kuɗi na Afirka na baya-bayan nan – zai sake farfaɗo da kuɗaɗen da aka kashe wajen gina matatar man Dangote da hada-hadar man fetur, babbar matatar guda ɗaya a duniya mai ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana”.
Bankin Afreximbank ya ba da gudunmawar dalar Amurka biliyan 1.35, kaso mafi girma a tsakanin bankunan da ke halartar taron, yana mai jaddada ƙudurinsa na samar da manyan ababen more rayuwa da ke ciyar da masana’antun Afirka gaba.
Tun lokacin da aka fara aiki a rukunin matatar a watan Fabrairun 2024, Afreɗimbank ya ci gaba da tallafawa matatar Dangote ta hanyar samar da manyan hanyoyin samar da kuɗaɗe — don samar da ɗanyen mai.
Aliko Dangote, Babban Jami’in Kamfanin Dangote, ya ƙara da cewa: “Gudunmawar Afreximbank ga wannan gagarumin tallafin kuɗi yana jaddada hangen nesa da muke da shi na bunƙasa masana’antar Afirka daga ciki. Wannan sake fasalin yana ƙarfafa mu wajen samar da albarkatun man fetur mai inganci a faɗin Afirka.
