Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Cocin Nijeriya (Anglican Communion) ta yanke alaƙa a hukumance da Cocin Wales bayan naɗin Bishop Cherry Vann, wani mai goyon bayan auren jinsi, a matsayin Babban Limamin Kirista na Wales.
Shugaban Cocin Nijeriya, Rebiran Henry Ndukuba ne ya sanar da hakan a yayin buɗe taro na 14 na Cocin Nujeriya na Chancellor, Registrars da kuma jami’an shari’a a Abuja ranar Talata.
Da yake kwatanta lamarin a matsayin “abin ƙyama,” Primate Ndukuba ya bayyana cewa shawarar ta saɓa wa sadaukarwar cocin ga koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ya kwatanta matakin da rabuwar Nijeriya da farko da Cocin Episcopal (Amurka) a 2003..
“Mun yi watsi da zaɓen Reverend Cherry Vann a matsayin Babban Limamin Kirista na Wales,” inji Ndukuba. “Kamar yadda muka yi a 2003, muna sake yanke duk wata alaƙa da lardin da ya rabu da gaskiyar Littafi Mai Tsarki.”
Duk da yanke alaƙar, Ndukuba ya nuna goyon bayansa ga mabiya ɗarikar Anglican a Wales, yana mai ba su tabbacin ci gaba da haɗin gwiwa ta hanyar dandamali kamar Global Anglican Future Conference (GAFCON). “Mu Cocin Nijeriya, tare da GAFCON, za mu tsaya tare da su,” inji shi.
Primate ya kuma bayyana shirye-shiryen faɗaɗa ayyukan cocin na duniya, tare da sabbin ayyuka da ake yi wa rajista a Jamus, Netherlands, da Finland. “Muna jin cewa Ubangiji yana kiran mu zuwa Turai don aiki,” inji shi.
