Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Jihar Katsina Malam Dr. Dikko Umaru Raɗɗa ya kai ziyarar bazata zuwa makarantar kwana ta maza dake garin ɓatagarawa don ganin yanayin makarantar da kuma ɗaliban.
Gwamna ya zagaya cikin makarantar sannan ya duba kitchen inda ake dafa abinci.
Da yake ɗaliban makarantar, gwamnan ya hore su da su zama mas ladabi da biyayya da kuma bin dokokin makaranta.
Wannan ziyara ta bazata ita ce ta farko da gwamnan Raɗɗa ya fara kaiwa domin gane ma idanunsa halin da ɗalibai ke ciki.
Ya kuma yi kira gare su da su himmatu wajen karatu domin zama shugabannin gobe.
Malam Dikko Raɗɗa ya duba ɗakin dafa abinci inda ya yaba da inganci da kuma tsabta na abincin da ake dafawa ɗaliban bayan ya ɗanɗana.
Ya yi wa ɗaliban albishirin cewa gwamnatin sa zata kara yawan kayan abincin da ake basu.
