Dikko Radda ya buɗe makarantar Family Support Programme a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya buɗe makarantar shirin tallafawa iyali da aka fi sani da Family Support Programme mallakan gwamnatin jihar.

Buɗe makarantar ya biyo bayan gyare-gyaren sashin raunin ɗalibai da sashin firamare, tare da saka kayan aiki wanda gidauniyar Oando ta samar.

Gwamnan ya yaba da gidauniyar Oando bisa ƙoƙarin da tayi na taimakawa harkan ilimi a jihar.

A cewar sa haɗaka da cibiyoyi masu zaman kansu da gwamnatin jihar zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalolin da ake fama da su a ɓangaren ilimi musamman a yankuna karkara.

Ya bayyana ilimi a matsayin ƙashin bayan cigaban kowace al’umma ” gwamnatin jihar Katsina na bakin ƙokarin ta ganin ko wane yaro ya sami ingantaccen ilimi a jihar.

A nata jawabin shugaban gidauniyar Oando Mrs Toni Uduimoh ta ce ɗaya daga cikin manufofin gidauniyar shine kawo cigaba a fannin ilimi a Najeriya.

Mrs Toni Uduimoh ta bayyana wasu daga cikin aikace-aikacen da suka haɗa da gyaran makarantu tare da samar da masu da kayan koya da koyarwa na zamani domin bawa ɗalibai damar fahimtar karatunsu.

By ukarofi