Daga USMAN KAROFI
A ranar Laraba, 5 ga Maris, 2025, jami’an ’yan sandan Najeriya sun tarwatsa wasu magoya bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da suka taru a ƙofar Majalisar Tarayya. Masu zanga-zangar sun hallara tun da misalin ƙarfe 8 na safe domin nuna goyon bayansu yayin da kwamitin Majalisar Dattawa kan ladabtarwa da ƙorafe-ƙorafe ke gudanar da wani taro.
Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga-zangar sun hallara ne a harabar Majalisar Tarayya domin nuna damuwa game da shari’ar da ake yi kan Sanata Akpoti-Uduaghan. Sai dai, jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa taron, don hana ɓarkewar rikici ko tada zaune tsaye.
Wannan lamari ya ƙara janyo ce-ce-ku-ce dangane da yadda hukumomi ke ɗaukar mataki kan masu zanga-zanga a Najeriya, musamman kan batutuwan da suka shafi ’yan siyasa da dokokin ƙasa. Ana ci gaba da jiran karin bayani daga hukumomin tsaro da Majalisar Tarayya kan lamarin.
