Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Bashin ƙasa, wato Debt Management Office (DMO) ta sake samun girmamawa a gasar Made-of-Africa Awards ta shekarar 2025 da ƙungiyar Musayar Hannayen Jari ta Nijeriya (NGX Group) ta shirya, inda ta karɓi lambar yabo ta musamman kan “Fice a Kasuwar Hannun Jari”.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi a Abuja, DMO ta bayyana cewa hukumar ta samu wannan yabo mai daraja karo na uku a jere, bayan nasarorin da ta samu a shekarar 2023 da 2024.
Sanarwar ta ce, wannan girmamawa ta jaddada muhimmancin rawar da DMO ke takawa wajen bunƙasa kasuwar hada-hadar kuɗi ta Nijeriya, musamman a fannin kasuwar hannun jari, waɗanda suka bai wa masu hannun jari dama daga kamfanoni da gwamnatocin jihohi.
Haka kuma, DMO ta ja hankalin masu zuba jari da dama, ciki har da na ƙasashen waje, ta hanyar bayar da takardun kuɗi na Gwamnatin Tarayya da kuma bin ƙa’idoji mafi kyau wajen gudanar da kasuwanni.
Hukumar ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da tsara sabbin dabaru da haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki domin ƙara darajar kasuwar bashi a matakin ƙasa da ƙasa.
DMO na ɗaya daga cikin hukumomin gwamnatin tarayya da ke kula da bashin Nijeriya, ciki har da bayar da shawarwari kan ɗaukar bashi, tabbatar da ɗorewar bashi, da kuma bayar da takardun bashi na gwamnati kamar FGN. Haka kuma, hukumar na kula da ingantaccen bayanan bashi da tsara dabaru don rage haɗarin bashi da kuɗin ruwa.
A ƙarƙashin jagorancin Daraktar-Gaba, Patience Oniha, DMO ta yi fice wajen inganta kasuwar bashi ta cikin gida, gabatar da bonds na dogon lokaci, da kuma fadada damar masu zuba jari.
Ta kuma jagoranci gabatar da kasuwar hada-hadar kuɗi domin tallafawa ayyukan ci gaban ƙasa, tare da tsara sabbin tsare-tsare domin inganta gudanarwa da ba wa masu zuba jari damar shiga kasuwa cikin sauƙi.
