Dokar Zaɓe ta 2026 na iya kawo cikas ga zaɓen 2027 — IPAC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Jam’iyyun Siyasa ta ƙasa, wato Inter-Party Adɓisory Council (IPAC), ta bayyana damuwa mai tsanani kan wasu matsaloli da ke cikin Dokar Zaɓe ta shekarar 2026, inda ta ce idan ba a gyara su cikin gaggawa ba, za su iya kawo cikas ga sahihanci da ingancin zaɓen shekarar 2027.

Shugaban ƙungiyar, Dakta Mamman Yusuf Dantalle, ya bayyana hakan ne yayin wani zama da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), inda aka tattauna kan dokoki da ƙa’idojin gudanar da jam’iyyun siyasa.

Ya jaddada cewa IPAC na da alhakin jan hankalin cikin gida da na ƙasashen waje kan gazawar da ke cikin tsarin dokokin zaɓe na yanzu, waɗanda ka iya raunana dimokuraɗiyyar da aka sha wahalar gina ta a ƙasar.

Ya ce duk da irin gudunmawar da ’yan ƙasa suka bayar a lokacin sauraron ra’ayoyin jama’a kan gyaran kundin tsarin mulki da dokar zaɓe, sabuwar dokar ta 2026 ba ta kai matsayin da ake fata ba.

A cewarsa, maimakon ta ƙara inganta tsarin dimokuraɗiyya, sai ta zama tamkar koma baya da ke buƙatar gyara cikin gaggawa domin kare muradun ƙasa.

IPAC ta kuma nuna damuwa kan yadda wannan dokar ce ta zama ginshiƙi wajen tsara jadawalin zaɓen 2027 da INEC ta fitar, lamarin da ta ce ya ƙara matsin lamba ga jam’iyyun siyasa, musamman waɗanda ba su cikin gwamnati, tare da takaita damar su na shirye-shirye yadda ya kamata.

Daga cikin muhimman buƙatun da IPAC ta gabatar akwai sake duba tanadin da ya tilasta amfani da tsarin zaɓen fidda gwani kai tsaye (direct primaries), inda ta nemi a dawo da zaɓen fidda gwani ta wakilai (indirect primaries). Ta bayyana cewa zaɓin yadda jam’iyya za ta zaɓi ’yan takararta lamari ne na cikin gida, bai kamata majalisa ta tsoma baki a ciki ba.

Haka kuma, ƙungiyar ta soki tanadin da ya tilasta wa jam’iyyun siyasa gabatar da rajistar mambobinsu tare da lambar katin shaidar ɗan ƙasa (NIN) cikin gajeren lokaci daga 1 zuwa 21 ga Afrilu, 2026, tana mai cewa hakan ba zai yiwu ba kuma zai ware mutane da dama daga tsarin siyasa.

IPAC ta kuma jaddada muhimmancin dawo da tura sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki kai tsaye daga rumfunan zaɓe zuwa dandalin INEC Result ɓiewing Portal (IReɓ), tana mai cewa wannan shi ne ginshiƙin gaskiya da bayyana gaskiya a zaɓe. Ta gargadi cewa kura-kuran da aka samu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 bai kamata su sake faruwa ba.

A ɓangaren hukunta laifukan zaɓe, IPAC ta nuna cewa sabuwar dokar na sassauta hukunci kan sayen ƙuri’u, abin da ke ci gaba da lalata sahihancin zaɓe. Saboda haka ta sake kira da a kafa Hukumar Laifukan Zaɓe domin hukunta masu laifi yadda ya kamata.

ƙungiyar ta kuma buƙaci Majalisar Dokoki da ta sake duba dokar gaba ɗaya cikin gaggawa, tare da kira ga abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa su yi amfani da tasirinsu na diflomasiyya wajen taimakawa bunƙasa dimokuraɗiyya mai ɗorewa a Nijeriya.

A nasa ɓangaren, shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa hukumar ta samar da sabbin ƙa’idoji domin inganta yadda jam’iyyun siyasa ke aiki da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana. Ya ce an sake fasalin dokoki daidai da sabuwar Dokar Zaɓe ta 2026 domin su dace da buƙatun zamani.

Ya ƙara da cewa, zaɓe mai inganci yana farawa tun daga matakin fidda ’yan takara, ba ranar zaɓe kaɗai ba. Saboda haka, sabbin ƙa’idojin za su taimaka wajen tabbatar da gaskiya, adalci da daidaito ga dukkan masu ruwa da tsaki.

A ƙarshe, ya buƙaci shugabannin jam’iyyun siyasa su yi amfani da damar wannan tattaunawa domin bayar da gudunmawa mai ma’ana, tare da haɗa kai wajen gina tsarin zaɓe da zai tabbatar da cewa kowace ƙuri’a tana da tasiri, kuma sakamakon zaɓe ba ya da shakku.

By ukarofi