2027: Komai tsananin adawa Tinubu sai ya sake lashe zaɓe – Uzodimma

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, zai sake lashe zaɓen 2027 duk da ƙalubalen adawa.

Uzodimma ya faɗi haka ne a taron yankin Kudu maso Kudu na ƙungiyar masu goyon bayan shirin “Renewed Hope” da aka gudanar a Asaba, inda ya ce sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke yi sun fara gyara tattalin arzikin ƙasa, duk da cewa jama’a na fuskantar wasu ƙalubale a halin yanzu.

Ya jaddada cewa wahalhalun da ake fuskanta na ɗan lokaci ne, yana mai kira ga mambobin ƙungiyar da su wayar da kan jama’a a matakin ƙasa da ƙasa kan manufofin gwamnati.

A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oboreɓwori, ya ce haɗin kai da ƙarfafa goyon bayan jama’a na da muhimmanci wajen nasarar jam’iyya, yayin da tsohon gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa, ya ce taron zai taimaka wajen inganta fahimtar manufofin gwamnati.

Mahalarta taron sun fito daga jihohin yankin Kudu maso Kudu, inda aka tattauna hanyoyin ƙarfafa goyon bayan jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027.

By ukarofi