Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a shekarar 2023, ya yi alƙawarin farfaɗo da masana’antun da ke Kano da dawo da bankin Arewa da aka fi sani da ‘Bank of the North’.
Obi ya yi waɗannan kalamai ne a ranar Lahadi a lokacin da ya kai ziyara gidan tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, a wani bikin sallah da Kwankwaso ya shirya wanda ya samu halartar ɗaruruwan mutane.
Obi ya halarci taron ne tare da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson.
A yayin da yake magana da ɗaruruwan jama’ar da suka taru, Obi ya shaida musu cewa duk da maƙasudin ziyararsa ita ce taya Kwankwaso murnar sallah ammma ya ba da tabbacin burinsa na farfaɗo da tattalin arziƙin Kano.
Ya kuma ce zai farfaɗo da masana’antun jihar da suka daina aiki domin ƙarfafa kasuwanci.
“Muna son kawo sauyi a Kano. Muna son gina sabuwar Kano. Abin da muke so shi ne dawo da ƙarfin da jihar Kano, dukkan masana’antu da ke Bompai, Sharada 1, Sharada 2, da bankin Arewa muna son farfaɗo da dukkan wadannan. Yau ba ranar siyasa ba ce, ranar bikin sallah ce,” inji Obi.
A cewar dokar zaɓe ta Nijeriya, za a fara yaƙin neman zaɓe ne a ƙarshen shekarar nan. Sai dai wannan ba zai hana mu amfani da taron sallah wajen isar da saƙonmu na siyasa ba.
Kwankwaso ya nuna wa manyan baƙin irin farin cikin da yake ciki tare da nuna farin cikinsa kan irin haɗin kan aka nuna a yayin bikin sallah.
Taron wannan shekara ya jawo hankalin al’ummar ƙasar nan saboda shi ne taro na siyasa na farko da Kwankwaso ya yi tun bayan da gwamnan Kano, Abba Kabir, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
‘Yan Kwankwasiyyar dai suna sanye da jajayen kaya a yayin da suka kai masa ziyara.
Siyasar Kano dai ta ɗauki wani sabon salo bayan da gwamnan Abba ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC wanda ya kawo ƙarshen tafiyar siyasa da suke tare.
Haɗuwar Obi wanda jigo ne a jam’’iyyar ADC da gwamna Makinde na jam’iyyar PDP a gidan Kwankwaso na nuna yuwuwar wani gagarumin shiri gabanin zaɓen 2027.
