Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar All Progressive Congress APC dake jihar Zamfara ta ƙalubalanci gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal da ya fito fili ya yi wa mutanen jihar bayani kan yadda ya kashe sama da Naira tiriliyan 1 da ya samu daga gwamnatin Tarayya a cikin shekaru biyu na gwamnatinsa.
Jam’iyyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran ta Yusuf Idris ya sanya wa hannu kuma aka bai wa Blueprint Manhaja a Gusau jiya Alhamis.
Za a iya tunawa ƙaramin Ministan Tsaro Hon. Bello Mohammed Matawalle a lokacin ziyarar da ya kawo jihar a makon da ya gabata ya ƙalubalanci gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal kan samun Naira tiriliyan 1 daga gwamnatin tarayya a shekaru biyu da ya yi akan mulkin jihar.
Jam’iyyar ta ƙalubalanci gwamna Dauda Lawal da cewar yana ɓoye abin da ya samu ko dai daga rabon tarayya ko kuma wanda aka samar a matsayin kuɗin shiga na cikin gida.
Jam’iyyar ta kuma bayyana matsalar a matsayin rashin gaskiya da riƙon amana daga gwamnatin gwamna Dauda Lawal.
“Matawalle, minista kuma cikakken memba na majalisar zartarwa ta tarayya tabbas yana da masaniya game da kuɗin da gwamnatin jihar Zamfara ta karɓa”.
A cewar sanarwar, kamar yadda tsohon gwamnan jihar Matawalle ya san yadda abin yake, a lokacinsa da kuma yadda ake zuba ƙarin kuɗi a cikin tsarin jihar ba tare da an cimma wani ci gaba ba.
Jam’iyyar ta umarci gwamnatin PDP a ƙarƙashin gwamna Dauda Lawal da ta buga bayanin abunda ke asusunta daga ranar 29 ga Mayu, 2023 tare da kuɗin da aka karɓa daga asusun tarayya, raba gwamnatocin jiha da ƙananan hukumomi.
“Wannan naira tiriliyan ɗaya ba ta haɗa da kuɗaɗen da hukumomin bayar da tallafi suka bayar ba, asusun dawo da cutar Corona, tallafin harajin ci gaban tarayya, asusun tallafin tsaro na Naira biliyan 10 na wata-wata da kuma asusun tallafi na cire tallafin kuɗi na biliyan 20 wanda yawancin ‘yan jihar ba su sani ba”.
“Waɗannan ma suna cikin ƙalubalen da muke fuskanta na gwamnati ta bayyana wa jama’a da kuma yadda Gwamna Dauda Lawal ya yi amfani da su”.
Jam’iyyar ta koka da yadda Gwamna Dauda Lawal ya kori ma’aikatan gwamnati sama da 3000 a lokacin da yake kan mulki a matsayin gwamna.
Ta jaddada cewa Matawalle ya tsara ɗaukar ma’aikata 1400 aiki, baya ga ɗaukar dubban mutane, ciki har da waɗanda aka naɗa a siyasa, domin samar da damarmakin aiki, ƙarfafa matasa da kuma samar da abinci ga iyalai.
Jam’iyyar ta gargaɗi gwamna Dauda Lawal cewa idan ya gaza buga asusun gwamnatin jihar Zamfara a Jaridun Kamar nan kamar yadda doka ta tanada a kowace shekara, jam’iyyar za ta yi amfani da Dokar ‘Yancin Samun Bayanai don neman a fitar da bayanan ta hannun banki.
