Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Sakataren tsare-tsaren Jam’iyyar APC ta ƙasa kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Kebbi Alhaji Sulaiman Muhammad Argungu ya jajentawa iyalan waɗanda harin makarantar ‘yan matan Maga ya shafa.
Ya bayyana cewa babu shakka akwai damuwa mai yawa saboda rashin sanin halin da waɗannan yaran da ‘yan bindiga suka sace sai dai babu yadda za a yi sai dai a cigaba da addu’ar Allah ya bayyana su ya kuma sada su da iyayensu cikin ƙoshin lafiya.
Ya kuma nemi iyaye da ‘yan uwansu da su ɗauki wannan abin a matsayin muƙaddari ne daga Allah wanda babu wani mahaluki da zai iya kaucewa ƙaddararsa.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati tana nan tana iya kokarin ta na ganin jami’an tsaro sun gano tare da mayar da su ga iyayen su cikin koshin lafiya in Sha Allahu.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu ya baiwa iyalansu haƙurin jure wannan rashin.
Ba shakka jinin su ba zai tafi a banza ba saboda sun mutu ne a bakin aiki ne.
