
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An shiga sabon fargaba a wasu sassan jihohin Adamawa da Borno bayan saƙon gargaɗin ankararwa da aka fitar game da shirin ƙungiyar Boko Haram na ƙaddamar da wasu hare-hare a ƙananan hukumomin Michika da Askira-Uba.
Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) ce ta fitar da saƙon, inda ta yi iƙirarin cewa mayaƙan ƙungiyar na shirin gudanar da atisayen hare-haren ne sakamakon zargin rushewar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da gwamnatocin jihohin biyu.
An gabatar da takardar saƙon ne mai ɗauke da kwanan wata 27 ga Yuli, 2026 ga Kwamandan Birget ta 23 ta Rundunar Sojin Nijeriya da ke Yola, Jihar Adamawa, wadda Daraktan Tsaron jihar, Ben Osifor ya sanya wa hannu.
A cewar rahoton leƙen asirin, ana zargin mayaƙan Boko Haram da kitsa kai hare-hare a yankin Michika da ke Adamawa da kuma Askira-Uba a Borno.
Wannan gargaɗi ya sake tayar da fargaba acikin al’ummar yankunan kan sabunta ayyukan ‘yan tayar da ƙayar-baya a shiyyar ta Arewa maso Gabashin Nijeriya.
A cewar rahoton ShaharaReporters, ankararwar ta DSS na zargin mayaƙan da shirya garkuwa da jami’an gwamnati, kansiloli, sarakunan gargajiya, jagororin addini da wasu mazauna a yayin ƙaddamar da hare-haren nasu.
Ya ƙara da cewa, dagacin Michika da ɗansa na daga cikin waɗanda ake fakwa idan aka je aiwatar da shirin. Haka kuma, mayaƙan sun tura tawagar tsegumi domin sanya ido a wuraren.
Akan haka ne hukumar ta yi kira ga jami’an sojoji da ‘yan sa-kai da su ƙarfafa tsaro a yankunan da ke fuskantar barazanar hare-haren, tana mai shawartarsu da su yi aiki tare da masu tsaron gandun daji da mafarauta domin samun nasarar daƙile shirin.
