DSS ta kama jami’an ‘yan sanda da na shige da fice bisa zargin hannu a dawowar El-Rufa’i Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS, ta cafke wasu jami’an tsaro guda biyar bisa zargin su da hannu a shirya dawowar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai daga Masar a ranar 12 ga Fabarairu.

Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an na DSS sun yi yunkurin kama shi a filin jiragen saman na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a lokacin da El-Rufa’in ya dawo Nijeriya amma hakan bai yi nasara ba.

Majiyoyi sun ce a lokacin DSS ta yi yunƙurin ne da nufin tsare shi tun a filin inda ya tirje da kafa hujja da cewa ba zai bi su ba ba tare da takardar gayyata ta musamman ba, saidai sun yi nasarar ƙwace masa fasfo.

DSS ta zargi wasu jami’ai da karɓar cin hanci domin sauƙaƙa masa shiga wuraren da aka haramta tare da hana aiwatar da hukuncin doka akansa.

Hukumar ta ce bayan tsananta bincike, jami’ai biyar sun amsa laifinsu kuma an miƙa su ga hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) domin gurfanarwa.

A halin yanzu, El-Rufai wanda ya amsa gayyatar EFCC, ya musanta zargin yana mai cewa ana yi masa farautar siyasa.

DSS ta bayyana cewa, za a hukunta duk wanda aka samu da laifi, ciki har da waɗanda suka yi amfani da muƙamansu ba bisa ƙa’ida ba akan al’amarin.

By Babaji