Ramadan: Gidauniyar Mai Turaka ta raba tallafin kuɗi na Naira miliyan 10 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Waɗanda suka amfana da tallafin kuɗin sun haɗa da shugabannin jam’iyar APC na mazaɓu a ƙaramar hukumar Katsina,masu unguwanni,mata,matasa da masu buƙata ta musamman a ƙaramar hukumar.

A jawabinsa kafin ƙaddamar da bada tallafin Gwamna Dikko Raɗɗa ya yabawa Abdul’aziz Mai Turaka da irin wannan na mijin ƙoƙari a cikin wannan wata mai alfarma.

Ya ce dama Mai Turaka ya saba hidimar al’umma wannan ba shine karo na farko ba.

Gwamnan ya kuma jinjina masa kan yadda ya faɗaɗa bayar da tallafin ya zuwa matakin ƙaramar hukuma wanda a cewar sa tallafin kuɗin bai tsaya a mazaɓar sa ne kawai a da.

“A na san irin wannan samu na Mai Turaka domin da ya damu to al’umma za kaga sun amfana,”inji Dikko.

Malam Dikko Raɗɗa sai yayi kira ga musamman matasa yan kasuwa da suyi koyi da Mai Turaka wajan tallafawa al’ummar.

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi amfani da wannan wata mai alfarma su sanya jihar Katsina cikin addu’ar samun zaman lafiya.

“Mu kuma shugabanni mu sanya Imani da tausayin talakawa wajen jagoranci,”inji Dikko Raɗɗa.

A jawabinsa sa shugaban Gidauniyar, Abdul’aziz Mai Turaka wanda kuma mataimaki na musamman ga Mataimakin shugaban majalisar Dattijai, ya yi godiya ga Allah ganin yadda ya faɗaɗa bayar da tallafin kuɗin daga mazaɓar unguwar sa ya zuwa matakin ƙaramar hukumar Katsina.

Ya ce wannan tallafin kuɗi ma somin taɓi ne domin a nan gaba zai fi haka in Allah ya yarda.

Ya kuma bayyana gwamna Dikko Raɗɗa a matsayin mutum mai gaskiya da hangen nesa ga kuma riƙon amana.

Mai Turaka ya yaba wa Dikko Raɗɗa kan irin aikace-aikacen raya ƙasa da ya kawo a ƙaramar hukumar Katsina.

Haka kuma ya yaba wa gwamnan kan yadda ya haɗa kan ya’yan jam’iyar APC mai mulki a jihar wanda ya ce ba a taɓa samun gwamnan da ya haɗa kan manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyar a duk faɗin ƙasa ba tare da ƙorafi ba “Amma Dikko Raɗɗa ya ci nasara haɗa kan kowa a jihar Katsina.

Ya bayyana nasarar da gwamnan ya samu na aikace-aikacen raya ƙasa a faɗin jihar da yadda yake tafiya da duk ya’yan jam’iyar APC ya sa in Allah ya yarda zai koma kujerar sa na mulki cikin ruwan sanyi.

By ukarofi