Kotu ta sanya 3 ga Maris don hukunci kan takardun EFCC a shari’ar Yahaya Bello

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Talata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ayyana 9 ga Maris a matsayin ranar yanke hukunci kan amincewa da wasu takardu da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta nemi gabatarwa akan shari’ar tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.

Mai shari’a Emeka Nwite ya ɗage zaman bayan muhawara mai zafi tsakanin lauyoyin ɓangarorin biyu kan sahihancin takardun kadarorin da ake son gabatarwa a matsayin

Shaida ta takwas a shari’ar, Gabriel Ochoche, wanda jami’in banki ne, ya shaida wa kotun cewa cikin. dukkan shigowa da fitar kuɗi da aka nuna masa, babu wanda ke da alaƙa da tsohon gwamnan.

Ya kuma bayyana cewa,
ba shi da wata alaƙa da asusun kamfanin Kumfayakum Global Limited da aka gabatar a matsayin hukk.

Ochoche, wanda jami’in bankin Wema ne, ya ƙara da cewa, bai iya gano Naira miliyan 100 daga kamfanin Keyless Nature Limited da ta shigo ba ta mece ce.

A cewarsa, masu asusun ne kaɗai za su iya fayyace dalilan karɓa ko aika kuɗi daga kamfanin.

Lokacin da aka tambaye shi ko ya san wanda ake tuhuma, sai ya amsa cewa ya san shi a matsayin tsohon Gwamnan Jihar Kogi, amma sunansa bai fito a takardun da aka nuna masa ba.

Shaida na gaba, Mahmoud Abdulazeez na kamfanin Ɗantata & Sawoe Construction, ya yi bayani kan wata kadara da ke Gwarinpa II, Abuja, inda aka ce an rattaɓa hannu kan Deed of Assignment tsakanin wasu ɓangarori.

Sai dai lauyan kariya, Joseph Duadu ya ƙalubalanci gabatar da takardun, yana mai cewa ba a nuna an yi musu rajista ba, don haka ba su cancanci karɓuwa a kotu ba.

Lauyan EFCC, Kemi Pinheiro (SAN), ya ce an gabatar da su ne domin ƙarfafa shaidar baki, ba don tabbatar da mallakar fili ba.

Kotun ta ɗage zaman zuwa 9 ga Maris, 2026, domin yanke hukunci kan sahihancin takardun tare da cigaba da sauraron shari’ar.

By Babaji