Waken soya da lafiyar fata: Kyau daga ciki zuwa waje

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja, sannunku da jimirin bibiyarmu. Ya ibada, Allah Ya karɓa daga gare mu.

A yau shafin zai waiwaye abincin da ke da tasiri a lafiyar fata wanda yake ɗauke da sinadarai da ke iya ba mu fiye da abinda muke samu a mayukan da muke siya da tsada.

Mutane da dama na mayar da hankali kan man shafawa da kayan kwalliya wajen neman fata mai haske da santsi. Sai dai masana sun tabbatar da cewa ainihin kyawun fata yana farawa ne daga ciki, wato daga irin abincin da ake ci da sinadaran da jiki ke samu.

Daga cikin abincin da bincike ya fi mayar da hankali a kansa akwai waken soya, wanda aka gano yana ɗauke da sinadarai masu amfani musamman ga fata.

Rahotannin bincike sun nuna cewa, sinadaran da ke cikin waken soya musamman waɗanda ake kira isoflavones, na taka muhimmiyar rawa wajen ƙara danshin fata, ƙarfafa ta, ƙara samar da sinadarin kolajin (wanda ke ba fata ƙarfi da taushi), rage layukan tsufa da kuma inganta katangar kariyar fata.

Isoflavones: Sinadaran da ke farfaɗo da fata

Isoflavones wasu sinadarai ne da ake samu da yawa a waken soya. Manyan nau’o’insu uku sun haɗa da genistein, daidzein da glycitein. Waɗannan sinadarai aikinsu na kama da aiki irin na sinadarin halitta na mata wanda ke taimakawa wajen kula da lafiyar fata.

Masana na ci gaba da nazarin su saboda an gano suna samar da sinadarin ƙarfafa fata, kare fata daga lalacewar yanayi, rage kumburi idan fata ta yi, da kuma taimakawa sabunta ƙwayoyin fata.

Masana sun bayyana cewa, raguwar sinadarin mata, musamman bayan daina jinin al’ada, na sa fata ta ragu a ƙarfi da danshi. Isoflavones na taimaka wa rage wannan tasiri. Wannan ya sa ake kallon su a matsayin ginshiƙai wajen rage tasirin tsufa.

By ukarofi