DSS ta miƙa wuya ta saki Shugaban NLC bayan ta ƙwace masa fasfo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar DSS amsa buƙatar NLC ta sako shugabanta, Joe Ajaero.

Ajaero, wanda aka sako shi wajen ƙarfe 12 na daren ranar Talata ya ce an sako shi ne kafin tsakiyar dare na ranar Litinin.

Shugaban na NLC ya ce, jami’an sun sako shi bayan sun ƙwace masa fasfo ɗinsa.

An kama Ajaero ne a jiya Litinin a lokacin da ya ke kan hanyar ficewa daga Nijeriya zuwa Landan a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

Hakan na zuwa ne bayan wani zama na gaggawa na rassan ƙungiyar ciki har da ma’aikatan wutar lantarki inda ta aika da sakon batun mika wuya kan sako Mista Ajaero cikin wata takarda da suka fitar.

By Babaji