Daga BASHIR ISAH
Hukumar tsaro ta DSS, ta ce ta ƙirƙiro da shafukan sohiyal domin bunƙasa hanyoyinta na hulɗa da jama’a da masu ruwa da tsaki.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukunar, Dr Peter Afunanya, ne ya bayyana hakan ranar Litinin a Abuja.
Ya ce shafukan da suka ƙirƙiro sun haɗa da:
Twitter: @OfficialDSSNG Facebook: OfficialDSSNG Instagram: @OfficialDSSNG
A cewarsa, shafin Tiwita na PRO na hukumar shi ne: @DrAfunanya_PNA.
Ya ce kafin wannan lokaci hukumar ba ta da waɗanan kafafe, kuma tana sa ran soma amfani da su ne daga ranar 6 ga Maris.
Jami’in ya ce al’umma su sani cewar, kafin wannan lokaci duka shafukan soshiya midiya da ake amfani da su da sunan hukumar na bogi ne.