
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa akan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Adeyemi Adaramodu ya bada sharuɗɗa waɗanda sai an cika su ne sannan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan za ta dawo bakin aiki.
Adaramodu ya bayyana hakan ne bayan wata babar kotu a Abuja ta yi hukuncin umarni dake neman a dawo da Natasha, wadda aka dakatar wattani kaɗan da suka gabata, inda ya ce majalisar ba za ta dawo Sanatar ba har sai ta nemi yafiya.
Ya ce, umarnin kotun ba zai hana yin aiki da dokokin majalisar ba wajen hora mambobinta.
A watan Maris ne majalisar ta dakatar da Sanata Natasha na tsawon watanni shida bisa saɓa wa dokokinta bayan samun tsama da shugaban majalisar, Godswill Akpabio akan tsarin zama a zauren majalisar.
Al’amarin ya yi ƙamari ne a lokacin da Natasha a wata hira da ɗaya daga cikin manyan gidajen telebijin na ƙasa, ta yi zargin Akpabio da ƙoƙarin cin-zarafinta, lamarin da acewarta rashin amincewarta akan haka ne ya sa ake musguna mata a majalisar.
Daga nan ne ta shigar wa kwamitin ladabtarwa takardar ƙorafi, inda ta yi zargin shugaban majalisar da ƙoƙarin cin-zarafin nata.
Daga bisani, ta ƙalubalanci dakatarwar da aka yi mata a babbar kotun.
