Shugaban SDP na Kaduna ya rasu a hatsarin mota

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar SDP a Jihar Kaduna ta shiga jimami a yayin da shugabanta a shiyya ta ɗaya, Alhaji Bashir Zakariya ya rasu a hatsarin mota, wanda ya auku a hanyar Zariya zuwa Kaduna.

An ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a lokacin da Zakariya ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Zariya.

Duk da cewa babu cikakken bayani game yadda al’amarin ya faru, wasu mambobin jam’iyyar sun tabbatar da cewa ya rasu ne a wajen da abin ya faru.

A sanarwar da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar a jihar, Darius Kurah ya fitar, SDP ta bayyana shugaban a matsayin wanda ya sadaukar da kansa wajen yi wa jam’iyyar da dimukraɗiyya hidima.

Ta kuma ce, rashinsa zai haifar da babban giɓi a gare ta inda zai yi wahala a samu wanda zai maye gurbinsa musamman duba da rawar da ya ke takawa wajen damawa da al’umma wajen ƙoƙarin gina siyasa ta gari.

Tuni jama’a suka fara kai gaisuwar ta’aziyya ga iyalansa a Kaduna.

By Babaji