
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Marubuta Labaran Wasanni (SWAN) ta bayyana kaɗuwarta bisa rashin tsohon mai tsaron gida na Super Eagles, Peter Rufai wanda ya shahara da sunan ‘Dodo Mayana’.
Shugaban ƙungiyar, Isaiah Benjamin a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja, ya bayyana Rufai a matsayin ɗaya daga cikin ƴan wasa masu kishi da suka sanya Nijeriya ta ke alfahari da su bisa nasarori da tarihin da ya kafa.
Bisa jajircewar da sadaukarwarsa ne ƙungiyar, wadda ita ce lamba ta ɗaya wajen harkar rubutun labarin wasanni, ta kirayi Gwamnatin Tarayya da ta samar da wani abu da zai zama dalili na a riƙa tunawa da marigayin.
Baya ga haka ne Benjamin ya kuma miƙa gaisuwar ta’aziyyarsa ga iyalai da ƴan uwa da abokan arziƙi da ɗaukacin fagen wasanni bisa rashin ɗaya daga cikin taurari ƙwallon ƙafa.
Ya kuma yi masa fatan samun rahama, a yayin da ake cigaba da jimamin rashinsa a Nijeriya da ma duniyar ƙwallon ƙafa.
