Shugaban gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya ya jagoranci tawaga zuwa ta’aziyyar Ɗantata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya jagoranci wata tawaga a yayin da suka kai gaisuwar ta’aziyyar rasuwar Hamshaƙin ɗankasuwar nan, wato Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata a Kano.

Babban ɗan marigayin, Alhaji Tajdeen Aminu Ɗantata da ɗaya daga cikin manyan ƙasa, Alhaji Sani Zangon Daura da wasu mambobin iyalan gidan ne suka ya karɓi baƙoncin tawagar gwamnan a gidansu dake Ƙoƙi a jihar.

A yayin jawabinsa, Gwamna Inuwa ya bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasa da ake ganin kimarsu a idon al’umma saboda halayensa masu kyau da ƙoƙarin kyautata wa al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.

A madadin sauran gwamnonin Arewacin Nijeriya, gwamnatin Gombe da ƴan jihar suna miƙa ta’aziyyarsu ga iyalan attajirin, kamar yadda ya bayyana.

Ya kuma yi addu’ar samun rahamar Allah ga mamacin gami da roƙa masa gafara da fatan ya zama ɗaya daga cikin waɗanda za su shiga Aljannar Firdausi.

Daga cikin waɗanda suka raka gwamnan akwai, Arch. Yunusa Yakubu, Dr. Jamilu Ishiyaku Gwamna, Alhaji Musa Garba, Muhammad Gambo Magaji, da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.

By Babaji