Tinubu ya isa taron BRICS a Brazil

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya isa Birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil domin halartar taron shugabannin ƙasashen ‘Global South’ da masu tasowa ta fuskar tattali karo na 17, waɗanda suka haɗa da Brazil, Rasha, Indiya, Chana da Afirka ta Kudu.

Ministan Afirka da Gabas ta Tsakiya na Brazil da Ambasada Carlos Sergio Sobral Duarte da mataimakin Ministan kasuwanci, kimiyya, fasaha, ƙirƙira da al’ada ne suka karɓi baƙoncin Tinubu.

Hakan ya biyo bayan gayyata ta musamman da Shugaba Luiz Inacio Lula Da Silva na ƙasar ya yi wa Tinubu a kwanakin baya.

Shugaban Nijeriyar zai halarci taruka mabanbanta a ƙarƙashin Lula a ranar 5 ga Yuli gabannin babban taron, wanda za a yi a ranakun 6 da 7 ga watan.

Sannan, Tinubu zai gabatar da jawabin ba’asi game da gyare-gyaren da ya ke yi wa harkar tattalin arziƙin Nijeriya da bayyana kyawawan manufofinsa domin janyo ra’ayoyin masu zuba jari.

By Babaji