Daga HABU ƊAN SARKI a Jos
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, yayin wata ziyara da ta kai Jihar Filato, ta sanar da bayar da tallafin zunzurutun kuɗi har Naira Biliyan ɗaya ga waɗanda ibtila’in hare-hare suka ɗaiɗaita a ƙauyukan jihar, domin su sake farfaɗo da rayuwar su.
An bayar da tallafin kuɗaɗen ne ƙarƙashin shirinta na Renewed Hope Initiative, wanda ke samun goyon bayan hukumomi da ƙungiyoyi masu zaman kansu. Sanata Oluremi Tinubu ta buƙaci al’ummar Jihar Filato su haɗa kansu, a daina kai wa juna hare-hare, domin jihar ta farfaɗo da cigaban da aka san ta da shi.
Da take magana a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jihar wanda aka gudanar a fadar gwamnati da ke Rayfield, Uwargidan Shugaban Ƙasar, ta shaidawa shugabannin ƙungiyoyin al’umma, sarakunan gargajiya, mata da matasa, cewa ta ziyarci jihar ne a matsayinta na uwa domin ta rarrashi ɓangarorin da ke rikici da juna, su yi haƙuri a samu zaman lafiya, a daina zubar da jinin da ake yi.
Ta ce, a duk lokacin da ta ji sabon rikici ko kashe-kashe a jihar, hankalinta yana tashi, don haka ta yi fatan nan gaba zuwan da za ta sake yi batun zaman lafiya da cigaba ne zai kai ta, ba na tashin hankali ba.
Ta kuma ja hankalin sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma su jingine bambancin siyasa ko na ƙabilanci, don samun haɗin kan jama’ar su, a samu dawo da zaman lafiya mai ɗorewa. Manoma su samu su koma gona, a samu wadatar abinci, yara kuma su koma makaranta, don ilimi ya inganta.
Sanata Oluremi Tinubu ta ce, “Bai kamata mu riƙa bar wa ýaýan mu gadon rikici da zubar da jini ba. Ya kamata zubar da jinin da ake yi a Filato ya kawo ƙarshe.”
Tun da farko, sai da Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ziyarci Gwamna Caleb Mutfwang a fadar gwamnatin jihar, inda ta jinjina masa da ƙoƙarin da yake yi na samar da sauye-sauye a jihar da ganin zaman lafiya ya koma kamar yadda aka san shi a baya.
Shi ma a jawabinsa, Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang ya yi mata tarba ta musamman tare da yi mata godiya game da yadda take nuna damuwa da halin da al’ummar jihar ke ciki, da kuma tallafin da take bayarwa, wanda ya ce yana taimakawa ainun wajen sauƙaƙawa jama’a halin da suke ciki.
Ya kuma ƙara ba da tabbacin ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi na ganin an inganta tsaro da walwalar al’umma, tare da kawo ƙarshen kashe-kashe da ake samu a jihar tsawon shekaru.
A madadin shirin Renewed Hope Initiative, Uwargidan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Hajiya Nana Shettima, ta miƙa gudunmawar buhunan shinkafa masu nauyin kg 50, har guda 1,800 ga matar Gwamnan Jihar Filato, Helen Mutfwang, don a raba wa gajiyayyu, mabuƙata, da nakasassu.
