Yadda Majalisar Dokokin Filato ta yi sabon kakaki

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

Majalisar Dokoki ta Jihar Filato ta zaɓi ɗan majalisa Naanlong Gapyil Daniel, mai wakiltar mazaɓar Mikang, a matsayin sabon Kakakin Majalisar, yayin da aka zaɓi ɗan majalisa, Isa Madaki Ajiji, mai wakiltar mazaɓar Jos ta Gabas, a matsayin Mataimakin Kakaki.

Wannan zaɓe ya biyo bayan ajiye aikin da tsohon Kakakin Majalisar, Rt-Hon Gabriel Dewan, ya yi ne wanda ya ce ya ɗauki matakin hakan ne bisa la’akari da tsarin karɓa-karɓa da siyasar jihar take amfani da shi, don haka ya ga dacewar ya sauka ya bai wa wanda ya fi cancanta ya hau.

An yi wannan zaɓe ne a wani zaman gaggawa da majalisar ta kira, inda ɗan majalisa mai wakiltar Tsakiyar Langtang ta Arewa, Nanbol Listic, ýa gabatar da sunan Sabon Kakakin a matsayin wanda za a zaɓa ya maye gurbin da tsohon Kakakin ya bari. Buƙatar da ta samu goyon bayan ɗan majalisa mai wakiltar Gabashin Mangu ta Arewa, Abdul Yanga. Nan take kuwa ɗaukacin ýan majalisar su 24 suka kaɗa masa ƙuri’ar goyon baya.

A jawabinsa na amincewa da zaɓen da aka yi masa, Sabon Kakakin Majalisar, Naanlong Daniel, ya yi godiya ga ýan majalisar da suka ga cancantarsa suka zaɓe shi ya shugabance su, tare da alƙawarin yin shugabanci na gaskiya da adalci.

Jim kaɗan bayan da majalisa ta kammala zaɓen ta, sai sabon Kakakin tare da rakiyar sauran ýan majalisar suka je fadar gwamnatin jihar, domin gaisawa da Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang, wanda ya yabawa ýan majalisar bisa yadda suka gudanar da zaɓen cikin lumana da natsuwa.

Ya ce, canji dole ne a rayuwar ɗan ‘Adam, a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Ya yi alƙawarin cigaba da yin aiki tare da majalisar, domin samun nasarar tafiyar da harkokin gwamnati a Jihar Filato.

Gwamnan harwayau, ya yabawa tsohon Kakakin da hali ya kamatan da ya nuna, domin cigaban tsarin dimukraɗiyya a Jihar, tare da yi masa fatan samun nasara a harkokinsa na siyasa nan gaba.

By ukarofi