
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tashar YouTube ta shahararren ɗan wasa Cristiano Ronaldo, wato UR Cristiano, ta kere ta wasu manyan taurari irin su Justin Bieber da Taylor Swift wajen samun mabiya.
Tun bayan buɗe ta a watan Agustan 2024, tashar ta karya tarihin da dama daga cikin tashoshi a kafar inda ta samu sama da mabiya miliyan 60 a ƙasa da wata guda da buɗe ta.
A watan Yulin 2025 ne tashar ta tara mabiya sama da miliyan 75, lamarin da ya mayar da ita ɗaya daga cikin tashohi mafi samun yawan mabiya a duniya.
Ana ganin hakan ya samu ne a sakamakon ɗinbin magoya baya da tauraro ɗan wasan ke da su a faɗin duniya.
