Edo: ‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da ɗan Chana bayan halaka jami’an Cibil Defens 8

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An sace wani ɗan Chana bayan kashe jami’an Hukumar Cibil Defens (NSCDC) su guda takwas a yankin Okpella da ke Ƙaramar Hukumar Etsako ta Kudu a Jihar Edo.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kuma raunata wasu jami’an NSCDCn guda huɗu da wani farin hula, waɗanda suke karɓar a wani asibiti.

Lamarin ya auku ne a lokacin da jami’an hukumar da aka tura aiki a kamfanin siminti na BUA da ke jihar ke rakiyar wasu ƴan Chana biyar bayan dawowa daga sintiri, a bakin shiga farfajiyar kamfanin.

Majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa ƴan bindiga sun kai wa tawagar jami’an farmaki ne ɗauke da wasu muggan makamai inda suka halaka guda takwas a nan take.

NSCDC ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda ranar Asabar.

Ta bayyana cewa, al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare a ranar Juma’a, 5 ga watan Satumba, 2025.

Tuni aka garzaya da gawawwakin mamatan wajen ajiyar gawawwaki yayin da kuma ake bai wa waɗanda suka jikkata magani.

By Babaji