Yan bindiga sun kashe mutum bakwai a Ɗandume

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan bindiga ɗauke da manyan makamai sun kai mummunan hari a ƙauyen Magajin Wando da ke ƙaramar hukumar Ɗandume inda nan take suka kashe mutane bakwai.

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya sanar da faruwar haka a wata takarda da ya fitar.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro na CWC suka kawo ɗauki a yayin da yan bindiga ke Kai hari a ƙauyen.
Haka kuma bayan da jami’an tsaron suka ɗauki waɗanda suka samu raunuka zuwa asibitin Ɗandume nan ma waɗannan ƴan bindigan suka sake tare su.

Sai dai bisa jajircewa, jami’an tsaron sun sami nasarar fatattakar ƴan ta’addan,koda yake an kone motar jami’an tsaron.

Dr Nasiru Ɗanmusa ya miƙa ta’aziya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu tare da jinjina wa jami’an CWC bisa jajircewa da ƙwarewa da suka nuna wajen fatattakar yan bindigan a ƙauyen.

Ya ce gwamnati za ta cigaba da aiki kafaɗa kafaɗa da sauran jami’an tsaro wajen kakkaɓe sauran yan ta’adda a jihar.

Yayi kira ga al’ummar jihar da su ba jami’an tsaro goyon baya ta hanyar bada sahihan bayanai da zai taimaka wajen yaƙar ta’addanci a jihar.

By ukarofi