Rikicin Kwankwasiyya: NNPP ta kori Hon. Abdulmumin Kofa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta sanar da sallamar Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa mai wakiltar mazaɓar Ƙiru/Bebeji a Majalisar Wakilai daga cikin jam’iyyar sakamakon ƙamarin rikicin cikin gida.

Hakan na zuwa ne yayin da ta zargi ɗan majalisar da yi wa jam’iyyar zagon-ƙasa, rashin biyayya da gaza sauke nauyin kuɗin jam’iyyar akansa.

Da yake ganawa da manema labarai a Kano, Shugaban jam’iyyar Hashim Sulaiman Dungurawa ya bayyana sukar jam’iyyar a fili da rikici tsakaninsa da takwarorinsa na siyasa ya sa NNPP ta ɗauki matakin akansa.

Hakan ya faru ne ƙasa da sa’o’i 24 da ɗan majalisar ya furta cewa ‘kada a yi mamaki matuƙar aka ga ya sauya jam’iyya’ domin matsayinsa ya kai ya yi hakan a siyasance, kamar yadda ya bayyana a wata hira da gidan talabijin nq Channels.

Dungurawa ya yi tir da kalaman na Hon. Kofa inda ya ce nasararsa a siyasa ta dogara ne da tafiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Da fari, jam’iyyar ta so shirya zaman sulhu da shi domin shawo kan matsalolin, inda daga bisani ta yanke hukuncin korarsa don kada ya ƙi amince wa zaman.

By Babaji