EFCC ta cafke ‘yan damfara 37 a Ekiti

Daga WAKILINMU

Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC) ta cafke wasu matasa 37 da aka fi sani da ‘yahoo-yahoo boys’ bisa zargin aikata damfara a intanet a Ado-Ekiti, jihar Ekiti.

Hukumar da kanta ta bayyana hakan a wata sanarwar manema labarai da ta fitar ta hannun Shugaban Sashen Yaɗa Labaranta, Wilson Uwujaren, a Litinin da ta gabata.

Sanarwar ta nuna EFCC ta yi nasarar kama matasan ne biyo bayan bayanan sirri da ta tattara kan harkokinsu na damfarar mutane ta intanet a yankin.

Hukumar ta ce sakamakon binciken da jami’anta suka gudanar a yankin, a nan ne suka gano maɓuyar ɓata-garin inda suka ɓoye suna cutar da jama’a.

EFCC ta ce biyu daga cikin waɗanda aka cafken, wato Dada Dele da Dada Tunde ‘yan gida ɗaya ne, uwa ɗaya, uba ɗaya. Sauran sun haɗa da; Segun Kazeem, Adepoju Pelumi, Jejelowo Segun, David Ojo, Sodiq Adetoye da kuma Opeyemi Akiniyi.

Sai kuma Sunday Adedoyin, George Tobi, Odunayo Daramola, Olubola Olushola Sunday, Temitope Ayomide, Faboro John Oluwagbotemi, Ajibade Timilehin Emmanuel sannan Momoh Ranti da sauransu.

Hukumar ta ce za ta gurfanar da waɗanda take zargin bayan ta kammala bincikenta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *