Ogun ta samu rigakafin korona guda 100,000

Daga AISHA ASAS

A Litinin da ta gabata Gwamna jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya karɓi allurar rigakafin cutar korona na AstraZeneca/Oxford guda dubu 50,000 a matsayin gudunmuwa daga Gwamnatin Tarayya.

Maganin ya shiga hannun gwamnan ne a ofishinsa da ke Abeokuta, jim kaɗan bayan dawowar tawagar da ta wakilci jihar ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr Tomi Coker.

Gwamnan ya shaida wa manema labarai cewa Ogun ita ce jiha ta farko da ta soma karɓar rigakafinta.

Yana mai cewa allura ƙwaya 50,000 da ta samu rukunin farko ne na abin da take sa ran samu baki ɗaya. Ya ce tsakanin Litinin da Talata, za su karɓi rukuni na biyu na maganin kwatankwacin na farko da suka samu.

Ya ce shi da mataimakinsa, Engineer Noimot Salako-Oyedele za su jagoranci yin rigakafin inda nan gaba kaɗan za a tsayar da ranar da za a yi musu allurar sannan sauran jama’a su biyo baya.

Sai dai gwmnan ya ja hankalin talakawansa kan su ci gaba da kula da matakan kariya, saboda a cewarsa rigakafin taimakawa kawai zai yi wajen rage kaifin cutar.

A cewarsa, “Za mu bada rigakafin ne ta hanyar la’akari da tsare-tsaren da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA) ta shimfiɗa. Hukumar ta lissafa wasu asibitoci (manya da ƙanana) a sassan jihar a matsayin cibiyoyin da za a yi amfani da su wajen bada rigakafin.”

Ya ce jami’an kiwon lafiya da dattawan jihar, su za a soma bai wa rigakafin kafin sauran jama’ar jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *