Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nijeriya, EFCC,Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta kama mutum 792 da ake zargi da aikata laifin damfara ta Intanet da suka gada da damfara ta hanyar soyayya.
An gabatar da wadanda ake zargin ne a ranar Talata, 10 ga watan Disamba, 2024, yayin wani samame da jami’an hukumar suka kai a maɓoyar wadanda ake zargin, a cikin wani katafaren gini dake lamba bakwai, Oyin Jolayemi Street, ɓictoria Island, Lagos, bayan hukumar ta samu bayanan sirri.
Da yake jawabi ga manema labarai, Olukoyede, a ranar Litinin, 16 ga watan Disamba, 2024, a ofishin hukumar dake Legas ya bayyana cewa cikin waɗanda aka kama akwai ‘yan Chana 148, da mutum 40 ‘yan ƙasar Filipinos da kuma ‘yan Kharzartans biyu, sai ɗan Pakistan da ɗan Indonesia.
Shugaban wanda ya samu wakilcin Diraktan hulɗa da jama’a na hukumar, CE Wilson Uwujaren, ‘yan ƙasashen wajen na amfani da ginin a matsayin wajen da suke koyar da ‘yan Nijeriya yadda ake damfara ta Intanet musamman ta hanyar soyayya, “ƙasa a cikin ginin an cika shi da manyan kamfutoci”, inji shi.
“A hawa na biyar, masu binciken sun gano layukan waya 500 da wayoyin sadarwa da aka tana da domin gudanar da ayyukan ta’addanci, ana amfani da ‘yan Nijeriyar wajen yaudarar ‘yan ƙasashen waje yawanci ‘yan Amurka da Canada da Meɗico da wasu ƙasashen Turai da dama.
