El-Rufai ya kwatanta dawo da Sarki Sanusi a matsayin abu mafi muhimmanci a rayuwarsa

Spread the love

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana matuƙar jin daɗin sa na mayar da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na 16.

El-Rufa’i ya bayyana haka a matsayin “Ɗaya daga cikin muhimman al’amura a rayuwata” a gare shi, inda ya bayyana muhimmancin wannan mataki.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata a wurin taron Arewa Tech Fest, taron da ya tattaro shugabannin siyasa da na fasaha domin tattauna ci gaban Arewacin Najeriya.

Bikin ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da Gwamnonin jihohin Kano, Katsina, da Zamfara.

“Mayar da mai martaba na ɗaya daga cikin muhimman al’amura a rayuwata kuma ina son sake taya ka murna”

An tsige Sanusi daga karagar mulki ne a shekarar 2020 a ƙarƙashin yanayi mai cike da cece-kuce. Wannan mataki dai ya sha samun ra’ayoyi mabambanta a faɗin ƙasar nan.

By ukarofi