
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Lauyan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya zargi Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) da yaɗa zarge-zarge marasa tushe akan El-Rufa’i na alaƙanta shi da wasu kadarorin biliyoyin kuɗaɗe a ƙasar Misra, yana mai bayyana ikirarin a matsayin wani ɓangare na siyasa.
A wata takarda da ya aike wa manema labarai a Abuja a yau Litinin kuma a madadin tsohon gwamnan, Lauyan mai suna Ubong Esop Akpan ya ce zarge-zargen an yi su ne ba tare da tabbatar da sahihancin hujjojinsu ba.
Ya bayyana cewa, an yada su ne don kare haramtacciyar tsarewar da aka yi El-Rufa’in, yana mai cewa hakan ba ya daga cikin binciken da ake gudanar akansa.
A cewarsa, El-Rufa’i ya kai kansa ofishin Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, a ranar 16 ga watan Fabarairu, inda aka bada belinsa a hukumance kana daga bisani aka garzaya da shi ofishin Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS inda ya shafe tsawon kwana biyu.
Sanarwar ta ƙara da cewa, tun a ranar 18 ga Fabrairu ne ake tsare da El-Rufa’i ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba kamar yadda doka ta tanada.
Haka kuma, lauyan ya ƙalubalanci halascin izinin tsare tsohon gwamnan da aka bayar a ranar 19 ga watan, yana mai ikirarin hakan ya ƙare a ranar 4 ga Maris, sannan ba a sanar da tawagar lauyoyin da ke kare shi ba dalilin cigaba da tsare shi ba a hukumance ba.
