Ina raye, inji ɗan hidimar ƙasa da aka sace yayin da ‘yan bindiga suka nemi sabuwar fansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan ɗan hidimar ƙasa ƙarƙashin Hukumar NYSC mai suna Musa Usman Abba da aka sace, ya sake aiko da wani bidiyo ta wayar masu garkuwa da shi, inda ya tabbatar cewa har yanzu yana raye.

A cikin bidiyon, Abba ya roƙi iyalansa da jama’a da su cigaba da ƙoƙarin ganin an kuɓutar da shi daga hannun ‘yan bindigar, waɗanda suak yi awon-gaba da shi tun a watan Junairu.

Rahotanni sun nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun riga sun karɓi kuɗin fansa na Naira miliyan 10, amma duk da haka suna cigaba da neman a ba su musu babura guda biyu kafin su sako shi.

Har yanzu dai ba a samu cikakken bayani daga jami’an tsaro ba akan halin da ake ciki yayin da ake cigaba da kira ga hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa domin ceto ɗan hidimar ƙasar.

Abba ɗalibi ne da ya kammala karatunsa na digirin farko a tsangayar Kimiyyar Tsirrai da Fasaharta daga Jami’ar Tarayya da ke Gusau, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 9 ga Junairu, 2026 a lokacin da yake kan hanyar tafiya Sakkwato daga Gusau.

By Babaji