Gwamnan Zamfara da mataimakinsa sun koma APC daga PDP

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal da mataimakinsa Malam Mani Muminu tare da mambobin majalisar zartarwa ta jihar sun sanar da shawararsa ta barin jam’iyyar PDP zuwa shiga jam’iyyar APC.

Mataimakin gwamnan jihar Malam Mani Muminu ya sanar da hakan a wata hira da manema labarai a ƙarshen taron masu ruwa da tsaki a gidan gwamnatin Gusau ranar Litinin.

“An yanke shawarar ne a taron masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati da ke Gusau, a daidai lokacin da rikicin cikin gida na PDP ke ƙara ta’azzara”. Ya ce.

Mataimakin gwamnan Malam Mani Mummuni ya bayyana cewa matakin na da nufin magance ƙalubalen tsaro da ci gaban jihar Zamfara, tare da daidaita ajandar “sabuwar fata” ta APC.

A cewarsa, masu ruwa da tsaki sun shawarci gwamnan da ya shiga jam’iyya mai mulki don samun kwanciyar hankali, ci gaba, da kuma ci gaba tare.

Mataimakin gwamnan ya buƙaci magoya bayansa da su yi rijista da APC, domin ƙarfafa ci gaban Jihar Zamfara.

“Shawarar ta nuna jajircewar Gwamna Lawal ga haɗin kai, kwanciyar hankali, da kuma hanzarta ci gaba ga Zamfara da Najeriya”. Ya ce

By ukarofi