Ellison ya sha gaban Musk a matsayin mafi kuɗi a duniya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Larry Ellison, wanda ya kafa kamfanin Oracle, ya samu ƙaruwar dukiya ta ban mamaki, inda a yanzu ta doke Elon Musk, ya zama mutum mafi arziƙi a duniya.

Larry Ellison ya samu wannan matsayi ne bayan hannayen jarin kamfaninsa sun yi tashin gwauron zabo a kasuwar hada-hadar hannayen jari a ranar Laraba.

Farashin kowane hannun jarin Oracle ya tashi da 40 zuwa dala 340, lamarin da ya sa darajar kamfanin ta haura zuwa dala biliyan 958 (kimanin tiriliyan N1,443.1).

A cewar rahoton Bloomberg Billionaires Indeɗ, wannan karin ya sa dukiyar Ellison ta kai $393bn (kimanin tiriliyan N591.9), inda ya zarce Elon Musk wanda ke da dala biliyan 384 (kimanin tiriliyan N578.4).

Wannan ya sanya Ellison ya shiga sahun gaba a jerin masu arziki na duniya, inda ya bar Musk a matsayi na biyu.

Hakan ya kuma sanya Ellison ya shiga gaban sauran attajiran duniya irin su Mark Zuckerberg na Facebook da kuma Jeff Bezos na Amazon.

Duk da cewa yawancin kuɗin Ellison yana fitowa ne daga kamfanin Oracle, yana da wasu kadarori da dama da yake samun kuɗi da su.

Yana da hannun jari a Tesla, tsibirin Lanai a Hawaii, tawagar tseren jiragen ruwa, da kuma gasar ƙwallon teburi ta Indian Wells.

Haka kuma ya taimaka wajen sayen Twitter (ɗ) inda ya zuba jarin dala biliyan 1 (kimanin tiriliyan N1.5) domin kyakkyawar alakarsa da Elon Musk.

Ellison ya taɓa zama a kwamitin Tesla daga 2018 zuwa 2022, kuma na lokacin sayen Twitter, ya amince da zuba jari ba tare da jinkiri ba.

Har ila yau, littafin tarihin Musk da Walter Isaacson ya rubuta, ya nuna cewa Ellison ya sha gayyatar Musk zuwa tsibirinsa na Hawaii domin tattaunawa da kuma hutawa.

Larry Ellison ya zama mutum mafi kudi a duniya bayan da darajara kamfaninsa ta ƙaru a kasuwar hannun jari.

Darajar Oracle ta karu ne saboda ƙaruwar buƙatar kamfanonin AI da ke amfani da sabis na gajimare, ciki har da OpenAI, masu tafiyar da ChatGPT.

Waɗannan sabis suna buƙatar manyan cibiyoyin sadarwa irinsu Oracle domin gudanar da ayyukansu. Wannan ƙaruwar buƙata ta aara darajar kamfanin da kuma dukiyar Ellison.

Larry Ellison mai shekaru 81 ya zama mutum mafi arziki a duniya bayan ya zarce Elon Musk, inda kamfanin Oracle ya shi damar limancin attajiran duniya.

By ukarofi