Elon Musk zai fita daga gwamnatin Trump

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ɗaya daga cikin jigo a yaƙin neman zaɓen Donald Trump, Elon Musk na shirin kammala aikinsa a ƙarshen wata Mayu.

Trump ya bayyana hakan ga tawagar ma’aikatansa a makon da ya gabata, inda ya ce Shugaban Kamfanin Tesla, wato Musk zai ajiye matsayin da aka ba shi a gwamnati.

A ranar 20 ga watan Junairu, 2025 Musk ya fara aiki a matsayin jami’in gwamnati na musamman (SGE), inda zai ajiye aikin a yayin da wa’adin nasa ya cika.

Sakatariyar yaɗa labaran Fadar shugaban ƙasar Amurka, Karoline Leavitt ta ƙaryata rahoton da ke cewa Music zai bar aikin ne bisa wasu dalilai, ta na mai cewa tun farko Trump da Musk sun amince akan Musk zai bar aiki a yayin da ya kammala aikin DOGE, wanda shiri ne da aka samar da shi don rage adadin kashe-kashen kuɗaɗen gwamnati.

Shugaba Trump ya yaba da gudunmawar da Musk ya bayar kasancewar sa ɗaya daga cikin manyan attajirai a ƙasar, musamman ganin yadda ya tallafa wa tafiyarsa a yayin yaƙin neman zaɓe.

By Babaji