Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Wani gasar ƙwallon ƙafa da wata cibiyar agaji da ake kira Maikaya Foundation a turance ke shiryawa na bana shekarar 2025 da ake ciki yazo ƙarshe inda ƙungiyar F.C Dogara da a ka fi sani da Scorpions F.C tayi nasarar ɗaukan kofin gasar bayan ta doke abokan fafatawar ta wato Golden-bridge da ci ɗaya da nema a bugun daga kai sai mai tsaron-gida wato fanareti a turance bayan kunnen-doki na ci 1 da 1 da suka tashi cikin mintina 90 na gwabzawar.
Wasan ƙarshen wanda aka buga a filin wasanni na birnin Keffi a ƙaramar hukumar Keffi a Jihar Nasarawa ranar Lahadi na mako da ake ciki ya haɗa kawunan masoya ƙwallon ƙafa da dama da magoya bayan ɓangarorin biyu daga ciki da wajen jihar baki ɗaya.
Wakilin mu ya rubuto cewa manyan baƙi da suka halarci wasan ƙarshen sun haɗa da shugaba kuma wanda ya kafa cibiyar ta Maikaya Foundation wato wani matashin ɗan siyasa mai suna Hon. Mohammed Musa Maikaya da tsohon kwamishinan labarai na jihar kwamaret Dogo Shama da mai taimaka wa gwamna Abdullahi Sule a harkokin matasa da ɗalibai wanda shine kuma mai kula da harkokin cibiyar Hon. Sani Shuibu da kodinetan yaƙin neman zaɓen gwamna Sule a shiyar Arewa ta Gabas a jihar alhaji Attajiri da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Keffi Hon. Mohammed Dikko da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC mai mulki a jihar kwamaret Dauglas Ataro da dai sauran jiga-jigai ‘ya’yan jihar.
Da yake tattaunawa da manema labarai jim kaɗan bayan an gabatar da kyaututtuka ga waɗanda su ka yi nasara, Hon. Mohammed Maikaya ya bayyana cewa gasar ƙwallon ƙafar wadda cibiyar nasa na Maikaya Foundation ke shiryawa shekara-shekara wannan na bana 2025 karo na biyar kuma cibiyar tana shiryawa ne da manufar farautar dinbin matasan jihar dake da bai wa na musamman a fannin wasanni musamman na ƙwallon ƙafar don tallafa musu a fannin da kuma tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a tsakanin su da jihar baki ɗaya.
Ya cigaba da bayyana cewa ” Haɗa kan al’umma suna daga cikin manufofin mu a cibiyar Maikaya Foundation, saboda haka muna ganin haɗa wasan wani dama ce gare mu domin bada tamu gudumawa wajen tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin jihar nan ta Injiniya Abdullahi Sule a fannin samar wa ɗinbin matasan mu abin yi da kuma tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da walwala a duka sassan jihar nan gaba ɗaya.
“Mun zaɓi wasan ƙwallon ƙafar ne domin mun lura shi yafi ja hankalin matasa kuma zamu cigaba da ɗaukan nauyin gasar har sai mun zagaya duka ƙananan hukumomin jihar nan 13 da yardar Allah.
“Zaku iya yarda dani cewa kowa dake nan a yanzu yana cikin farin ciki da annashuwa sakamakon wasan nan, wannan shine burin cibiyar Maikaya Foundation a taƙaice.” Inji shi.
Ya kuma buƙaci matasa su guji zaman kashe wando maimakon haka su riƙa sa kansu a abubuwa da zasu bayyana baiwan su ga duniya kamar ƙwallon ƙafar don samun damar dogara da kawunan su nan gaba.
Daga karshe sai Hon. Mohammed Musa Maikaya yayi amfani da damar inda yayi kira ga hukumomi da suka dace a fannin na wasanni da masu ruwa da tsaki a jihar ta Nasarawa baki ɗaya su haɗa kai da cibiyar don tabbatar matasa sun samu abin yi a duka matakai don kauce wa ayukan ta’addanci da sauran munanan ɗabi’u tsakanin su da cigaban tattalin arzikin jihar baki ɗaya.
Abubuwa da aka gudanar a yayin wasan ƙarshen sun haɗa da gabatar da kofin gasar da kyaututtuka da lambobin yabo na musamman ciki har da tsabar kuɗi ga waɗanda suka zo na ɗaya da na biyu da kuma na uku kana aka kuma ɗauki hotuna da sauran su.
