
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu ƴan bindiga sun farmaki masallata a wani masallaci da ke Ƙauyen Marnona a Ƙaramar Hukumar Wurno ta Jihar Sakkwato, inda suka halaka mutum ɗaya da raunata wasu da dama.
Lamarin ya auku a yayin sallar asubahi, wanda ya haifar da tsoro acikin al’ummar yankin da ke gabashin jihar.
Wani shaida ya ce maharan sun je yankin ne ɗauke da wasu muggan makamai, inda suka yi ta harbe-harbe, lamarin da ya sa masallata suka fara tsere wa rayukansu.
Da ya ke tabbatar da aukuwar al’amarin, Shugaban jam’iyyar APC a jihar, Hon. Isah Sadeeq Achida ya yi alla-wadai da harin.
Ya kuma yi kira da a gaggauta farauto waɗanda ke da hannu a faruwar al’amarin don su fuskanci hukuncin doka.
Haka kuma, ya tabbatar da cewa, gwamnatin jihar da hukumomin tsaro suna aiki wajen ganin an daƙile ayyukan ta’addanci da suak addabi al’umma a sassan jihar.
Kazalika, ya jajanta wa iyalan waɗanda abin ya rutsa su da fatan samun waraka da wuri ga waɗanda suka jikkata.
