Bauchi: Zanga-zanga ta ɓarke a makarantar poly bayan harin dare a ɗakunan kwanan ɗalibai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An dakatar da harkokin karatu a makarantar Polytechnic ta Tarayya da ke Bauchi, bayan wata zazzafar zanga-zanga ta ɓarke sakamakon wani fashi da aka yi a ɗakunan kwanan ɗalibai maza da ya yi sanadin raunata da dama da sace wasu ababe masu tsada.

Lamarin ya auku ne a daren Litinin wayewar Talata, inda ƴan fashi suka kutsa cikin gidan tare da kwashe wayoyi da wasu kayayyakin karatun ɗaliban.

An ruwaito cewa, kimanin ɗalibai tara ne suka samu raunuka, waɗanda aka garzaya da su Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Ɓalewa (ATBUTH) domin yi musu magani.

An fara zanga-zangar ne cikin lumana da safe a babban titin Bauchi zuwa Dass, inda ɗalibai suka riƙa nuna ɓacin ransu da bayyana hakan a matsayin gaza ba su kariya daga makarantar.

Ana tsaka da haka ne sai ta rikiɗe zuwa tarzoma a yayin da wasu ɓata-gari suka shiga sahun masu zanga-zangar tare da yunƙurin hargitsa dandazon.

Daga nan ne jami’an ƴan sandan da aka tura wajen suka gaggauta fesa barkonon tsohuwa, inda su kuma ɗaliban suka riƙa jifa da duwatsu yayin mayar da martani.

A wata sanarwa daga Rajistiran Poly’n, Kasimu Salihu an tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce tuni suka umarci baki ɗaya ɗaliban da su fice daga farfajiyar makarantar har sai an kira su.

By Babaji