
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ƴan sanda a Jihar Kaduna, ta musanta rahotannin farko da aka fitar da ke cewa an rasa rayuka da dama a hatsarin tankar mai da ya faru a Ɗan Magaji na yankin Zariya.
A madadin haka ta ce, mutane da dama ne suka samu raunuka.
Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe a kusa da makarantar Rochas Foundation School da ke babbar hanyar Kaduna zuwa Kano, wanda ya rusta da tankokin mai biyu da motocin Volkswagen Golf biyu.
Kakakin ƴan sandan, DSP Mansir Hassan a wata ganawa da manema labarai, ya ce babu ran da aka rasa a hatsarin, saidai an garzaya da dukkanin waɗanda iftila’in ya rutsa da su asibiti.
Wata majiya ta shaida wa Blueprint cewa mutane huɗu sun jikkata kuma a halin yanzu suna karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello a Zariya.
Ta kuma ce, an faka motar Golf ɗin ne a gefen hanya a lokacin da wata tanka ta kutsa mata bayan karya dokar alamar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa.
