
Daga BELLO A. BABAJI
Fadar Vatican a ƙasar Italiya, ta sanar da ranar rantsar da sabon Fafaroma da aka zaba, Pope Leo na XIV, wanda za a yi a ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu, 2025 a Saint Peter’s Square.
Shugabannin duniya daga bangarori daban-daban ake sa ran za su halarci taron, kwanaki goma bayan zabar ba’amurke na farko, Robert Francis Prevost a matsayin shugaban kristocin darikar katolika na farko mai mabiya biliyan 1.4 a fadin duniya.
A ranar Juma’a ne Fafaroman zai gana da ƴan jaridu da ƴan difulomasiyyar Fadar da nufin gabatar da jawabi jawabinsa na farko.
Haka kuma za a yi hira da shi ta musamman a ranar 21 ga watan Mayu, 2025 sannan kuma zai gana da mambobin Vatican a ranar 24 ga watan.
A ranar 8 ga watan ne aka zabi haifaffen Amurkan, wanda ya zabi sunan Leo na XIV.
