
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Fenerbache dake kasar Turkiyya, Ali Koc ya haddasa cece-kuce acikin magoya bayan kwallon kafa, biyo bayan kalamansa akan dan wasan Super Eagles, Victor Osimhen.
A cewarsa, dan wasan, wanda ke buga wa babbar abokiyar hamayyarsu Galatasaray, ya fi karfin buga wasa a kungiyoyin kasar.
Ya ce, Osimhen dan wasa ne na musamman wanda sau daya ake samun irinsa a shekera 40.
Magoya bayan Fenerbache sun soki Shugaban kungiyar bisa rashin sayen dan wasan kafin Galatasaray ta saye shi.
Ya kare kansa da cewa ba a bai wa kungiyar tasu damar sayan dan wasan ba a lokacinda suak yi kokarin sayen sa, haka kuma akwai wasu dalilai da suka hana su sayan shi.
